Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Italiya Ta Dauki Mataki Kan Kungiyar Da Ke Tilasta Wa Matan Najeriya Karuwanci


A ranar Litinin din da ta gabata ‘yan sandan kwastam na kasar Italiya suka tarwatsa wata kungiyar ‘yan fatauci ta Najeriya da ta tilasta wa mata da dama yin karuwanci da bara a kan titunan kasar Italiya.

Sun kuma yi safarar miliyoyin Yuro na kudaden da ba su dace ba zuwa Najeriya, tare da boye wasu kudade a cikin akwatuna ko fakitin taliya.

Rundunar ‘yan sandan ta ce samamen da aka kai a garuruwan da ke arewaci da kudancin Italiya da kuma tsibirin Sardinia yayi sanadiyar kama mutane 40. Wadanda ake zargin dai ana tsare da su ne domin gudanar da bincike a kan zargin karkatar da kudade, da shige da fice ba bisa ka’ida ba, safarar mutane, jefa mutane cikin bauta da kuma karuwanci.

Wani abin da ya taimaka wajen tayar da binciken shi ne korafin wata ‘yar Najeriya da aka shigo da ita kasar Italiya ba bisa ka’ida ba, na cewa wasu yan kasarta na karbar basussukan da ya kai Euro 50,000 (dala 56,000) don su shigo da su, daga nan sai kawai aka tilasta musu yin karuwanci ga kungiyar. Ko da shike karuwanci ya halatta a Italiya, cin zarafin karuwai ya sabawa doka.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce yayin da kungiyar masu aikata laifuka ta Najeriya ke da sansani a kasar Italiya, ayyukanta ya kai kasashen Jamus da Libya da kuma Najeriya.

“An tura mata 41 zuwa karuwanci, yayin da tara aka tilasta musu yin bara,” in ji sanarwar.

Don hana matan zuwa hukumomi don neman taimako, "ana zaluntan su, ta hanyar amfani da tsafi na ibada don ba da tabbacin za su biya basussukan tafiya, in ji 'yan sanda.

A cikin 'yan shekarun nan, wasu matan 'yan Najeriya da aka tilasta musu yin karuwanci zuwa Italiya sun shaida wa hukumomi da ma'aikatan jin kai cewa ayyukan tsafin ya sa su ji tsoron cewa inda har suka saba zai haifar da mummunar bala’i ga iyalansu.

Masu laifin sun yi amfani da tawagogi 11 na masu aikewa da kudade, wadanda a wasu lokuta sukan boye makudan kudade a cikin hannayen jakunkuna ko a cikin fakitin taliya don gujewa bincike a filayen jirgin saman Italiya, in ji 'yan sanda.

XS
SM
MD
LG