Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Sun Yaudare Ni Zuwa Turai Don Tilasta Ni Karuwanci"


Bakin Haure daga Afrika
Bakin Haure daga Afrika

Hukumar yaki da safarar dan Adam a Najeriya ta fara wani aikin maidowa da kuma tsugunar da matan da aka yaudaresu zuwa Turai, inda aka tilasta masu aikin wahala da kuma karuwanci bayan an shigar da su Turai ta barauniyar hanya da sunan za a sama masu yayyuka masu albashi sosai.

Dubban matan Najeriya ne aka yi safararsu a cikin ‘yan shekarun nan, sai dai wasu a cikinsu sun dace har sun dawo gida su na sake gina kansu.

Ga Beatrice ‘yar shekaru 35, ba abu mai yiwuwa ba ne ta kauce ma yaudarar. A 2013 masu safarar mutanen sun ce za su sama ma ta aiki da albashi mai tsoka a wata babbar gona.

Beatrice ta amince da wannan yaudarar saboda a tunaninta za ta fitar da iyayenta daga talauci ta wajen aiki a kasar waje.

Tace, a maimakon haka, bayan an shigar da su Italiya ta barauniyar hanya mai cike da kasada da kuma wahala, sai aka tilasta ta yin karuwanci don ta samu kudi ta biya wadanda suka kai ta Turai.

Beatrice tace abokinta ne ya bata wannan shawara kuma yace mata zata yi aiki ne a cikin gona amma ba karuwamci ba kuma sai ta amince tace zata jarraba, amma bayan an bi dasu ta Libya kana suka dau jirgin ruwa wasu mutane da dama suka mutu a cikin jirgin, sai aka tilasta ta yin karuwanci.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mata sun haura rabin adadin dubban mutane da ake shigar da su Turai daga nahiyar Afrika ta barauniyar hanya a kowace shekara.

Amma kuma akwai maza ‘yan Najeriya da su kuma ake safararsu kuma ana tilasta su yin ayyukan karfi.

Chukwuemeka Asiegbu dan shekaru 45 da haifuwa ya kwashe shekaru shida a Libya, kuma da kyar ya sha. Yayin da ya dawo gida Najeriya ya kafa wata kungiya mai fafutukar kare ‘yancin mutane da aka yi safararsu.

Da taimakon hukumar yaki da safarar dan Adam a Najeriya ta NAPTIP, wadanda aka yi safararsu kamar su Beatrice za su fara sabuwar rayuwa bayan an ba su horon sana’o’in hannu. Yanzu haka Beatrice ta bude wurin sayar da abinci a gida Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG