Ma’aikatan wayar da kan jama’a na kasar Italiya sunce akwai babban sauyi ga yadda bakin hauren Afirka ke shiga kasar, inda ake ganin cewa mafi yawan ‘yan mata daga cikinsu duk daga Nigeria suke fitowa, kuma suna zuwa ne da sanin cewa karshenta zasu karkare ne a matsayin karuwai.
Amma yawancin ‘yan matan basu da masaniyar yadda halin rayuwarsu zasu kasance da wahalhalun da zasu fuskanta, da kuma tsawon lokacin da zasu kwashe kafin su gama biyan mutanen da sukayi fasa kwaurinsu zuwa Italiya.
A cewar wata bakuwar haure daga kasar Ghana, Appiah, kadan daga cikin ‘yan matan sukan tsira daga yin karuwanci, ta kuma ce tasan ‘yan mata hudu da suka kubuta a shekaru hudu da suka gabata, biyu daga cikinsu sun kwashe shekaru masu yawa suna karuwanci domin tara kudin da zasu biya íyayengijin na su, sauran biyun kuma sun sami tserewa zuwa kasar Jamus.
Jami’an Italiya da na Turai sun yi kiyasin cewa anyi fasakwaurin yara mata daga Najeriya masu shekaru daga 16 zuwa 17 har 16,000 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Facebook Forum