Wata mai horas da matasa a Nijeriya, Hajiya Hauwa liman, ta ce abin da ke haddasa fataucin bil’adama shine wasu na ta’alaka abin da talauci da rashin aikin yi saboda mafi yawan su na tafiya kassashen waje ne saboda neman rayuwa mai kyau.
Ta kara da cewa yawancin matasan da suka sami kauwunansu cikin matasalar rashin isashshen ilimi, basa samun ayyukan yi, ta dalilin haka ne wasu da dama musamman mata kan tsinci kawunansu cikin karuwanci.
Hajiya Hauwa ta yi karin bayyanin cewa wasu da ake fataucin su suna sane da abin da za su je yi a kassashen waje, wasu kuma basu da masaniya.
Kakakin hukumar yaki da fataucin mutane ta Najeriya, ya yi karin bayani akan karin wasu matakan da suke dauka dan shawo kan lamarin, kamar wayar da kawunan jama’a akan akan illar fataucin mutane ta haramtacciyar hanya.
Daga karshe ya bayyana cewa hukumar nada alakar aiki tare da Nahiyar Turai da Amurka domin shawo kan wannan lamari, kuma a cewarsa kwalliya na biyan kudin sabulu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Facebook Forum