Shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya, Kwamarad Ayuba Waba, yace akwai badakalar da aka tafka alokacin sayar da hukumar samar da hasken wutar lantarki ta Najeriya, abinda bincike kadai ka iya bankadowa. Inda yace, “yakamata a bincika domin wasu mutane ne kalilan, wanda basu da masaniya kan harkar wutar suka sayarwa kansu wannan albarkatu….”
Ko a yan kwanakin nan sai da wani dan Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Mohammed Hassan, ya koka bisa irin makurdan kudaden da aka zuba a harkar wutar lantarki a kasar, amma har yanzu kasar na cikin duhu, har ma ya nemi majalisar kasar ta kudanar da bincike.
Sai dai a cewar shugaban kungiyar rundunar adalci ta Najeriya, Alhaji Abdulkarimu Daiyabu, na ganin cewa matsalar wutar lantarki itace makasudin duk wata masifa a Najeriya.
Muryar Amurka tayi kokarin jin ta bakin ‘yan kasuwar da suka saye kamfanonin samar da hasken wutar lantarkin amma yaci tura, abin jira a gani shine yadda za a bude babin binciken da masu sharshi ke cewa ka iya bankado abubuwan mamaki.
Domin karin bayani.