Tun bayan hawan wannan sabuwar gwamnati aka fara binciken kudade sama da dala biliyan 2.1 da ake zargin an karkata akalarsu.
Kudaden an ware su ne domin sayen makaman da za a yaki kungiyar Boko Haram, lamarin da ya cutura.
A baya aka kama tsohon mai baiwa shugaba shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki wanda ake zargi kudaden sun fita daga ofishinsa.
Wannan badakala ta ja hankula mutanen Najeriya da dama ganin irin yawan kudaden da kuma irin halin tsananin rayuwa da mutane arewa maso gabashin Najeriya suka shiga, tun bayan da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a yankin.
Saurari wannan rahoto na Hassan Maina Kaina domin karin bayani: