Sa’oi kadan bayan da Amurka ta yi karin kudaden haraji daga kashi 10 zuwa 25 cikin 100 akan kayayyakin kasar China da ake shigowa da su Amurka, a yau Jumma’a shugaban Amurka Donald Trump ya yi ta aika sakkoni ta dandalinsa na Twitter, yana magana akan lamarin.
A daya daga cikin sakkonin, shugaban ya rubuta cewa, “mun yi shekara da shekaru muna asarar makudan kudade da ba zasu gaza dala milyan dubu 500 ba a cudanyarmu ta kasuwanci da China. Daga yau, wannan ta kare.”
Da take maida martini akan matakin a yau Jumma’a, gwamnatin China ta bayyana “takaicin ta”, ta kuma ce ita ma tana nan tana nazarin ramuwar gayyar da za ta yi wa Amurka.
Sai dai China ba ta bayyana irin matakan da take tunanin dauka ba.
Facebook Forum