Daga shekarar alif dari tara da tamanin da biyar (1985) zuwa shekarar alif dari tara da casa’in da hudu (1994), kamfanonin Donald Trump sun yi asarar dalar Amurka sama da biliyan daya, al'amarin da ya sa Trump, gabanin zamansa shugaban kasa, ya iya kauce ma biyan haraji na tsawon shekaru daga adadin shekaru 10, bisa ga wani rahoton jaridar New York Times a jiya Talata.
Trump ya kan bayyana kansa a matsayin kwararren dan kasuwa mai cin gashin kansa, kuma kwararre a harkokin kasuwanci.
To amma ya yi shekara da shekaru ya na ta asarar kudade, fiye da kowane mai biyan haraji a Amurka, a cewar jaridar ta Times, wadda ba ta yi amfani da ainihin bayanan takardun harajinsa ba, amma ta yi amfani da bayanan da wani wanda ya ga takardun ya gaya ma ta.
Facebook Forum