Kwamitin da ke kula da fannin tattara bayanan sirri a Majalisar Dattawan Amurka, ya bukaci babban dan shugaba Donald Trump ya bayyana a gaban kwamitin, don amsa tambayoyi da suka shafi tambayar da aka taba yi mishi a shekarar 2017, a wani yunkuri da kwamitin ke yi na binciken shisshigin da Rasha ta yi a zaben da ya gabata.
Kwamitin dai ya sake maida hankalinsa kan babban dan na Trump ne, bayan da tsohon lauyan shugaba Trump Michael Cohen, ya fadawa wani kwamitin majalisar wakilan Amurka cewa, ya zanta da dan shugaba Trump akalla sau 10, akan shirin gina Otel din Trump Tower a birnin Moscow.
Dan shugaba Trump ya taba shaidawa kwamitin na majalisar Dattawa a shekarar 2017 cewar, ya taba jin batun gina Otel din ne sama-sama.
Facebook Forum