Gwamnatin tarayyar Najeriya a yau Laraba ta kara farashin kudin Man fetur daga Naira 86 zuwa Naira 145, kowace, karamin Ministan Mai Mrs. Ibekachukwu,shine ya bayan haka.
Yace Gwamnati tayi juyayin daukar wannan matakin amma tilas ne ta dauke shine ganin irin wahalolin da kalubalen da kasar ke ci gaba da fuskanta duk da yunkurin da ake yi a lokuta daban daban na taimakawa farshin Man ya daidaitu kamar yadda aka san shi.
Ya kara da cewa hukumar dake kula da farashin Mai PPRA,ta bashi tabbacin cewa daga yau 11. Ga watan Mayu na 2016, zata fitar da sabon farshin Man fetur wand aba zai haura Naira 145, ba a kowace lita.
Daya daga cikin masu shigo da Mai Alhaji Abdullahi Idris, yace wannan shawarar da dace domin an kai matsayi dole ayi haka domin idan ba’a yi haka ba, ba za’a iya wadata Najeriya da Mai ba.