Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da rundunar ta ceto wani matashi a unguwar Sheka da aka daure tsawon shekaru.
A ranar Alhamis din data gabata ne ‘yan sanda suka ceto matashi na farko wanda mahaifin sa Malam Aminu ya daure tsawon shekaru bakwai a cikin wani daki a gidan sa dake Unguwar Farwa a gefen birnin Kano.
Yanzu haka dai mahaifin wannan yaro wato Malam Aminu da matarsa na shalkwatar ‘yan sanda a Kano suna fuskantar bincike, inda har ma kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Haruna Abdullahi ya ce, sakamakon farko na binciken su ya nuna tuhumar yunkurin kisan kai a kan Malam Aminu wanda dan Asalin garin Okene ne a can jihar Kogi.
Sai dai ga alama, kungiyar Human Rights Network wadda itace ta tseguntawa ‘yan sanda halin da wannan yaro ke ciki bayan da ta samu bayanan sirri, ta nuna rashin gamsuwa akan yadda ake kula da lafiyar Aminu Ahmed a Asibitin kwararru na Murtala a nan Kano.
Hakan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da ‘yan sandan na Kano ke cewa, sun ceto matashi na biyu dake fuskantar makamanciyar ukubar da Ahmed Amin ya fuskanta kuma suna ci gaba da bincike.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti
Facebook Forum