A karshen makon da ya gabata aka rika yayata wani hoton bidiyo da ya nuna wani yaro da ake zargin cewa mahaifinsa ya daure shi a turken dabbobi na tsawon shekaru biyu zargin da mahaifin ya musanta.
Shirin Domin Iyali ya yi tattaki zuwa inda wannan lamarin ya faru, domin jin ta bakin masu ruwa da tsaki a wannan batu da suka hada da 'yan fafatuka, mahaifin yaron, da kuma hukumomi.
A yau shirin ya fara da yada zango a hukumar kare hakkin bil'adama reshen jihar Kebbi , kungiyar da ta shiga gaba wajen kai wannan batu gaban hukuma.
Saurari bayanin da shugaban hukumar Barrista Hamza Attahiru wala ya yi wa wakilinmu Muhammadu Nasir.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.