Hakan ya biyo bayan kukan da kamfanonin sukayi na cewa sun kasa samun kudadensu da ya kai zunzurutun kudi Dala Biliyan Biyar, kamfanonin dai sun kai kukansu ne kungiyar jiragen sama ta duniya inda suka nemi da a matsawa Najeriya ta biyasu kudadensu.
Kawo yanzu dai matakin da babban bankin Najeriya ya dauka ya shafi musayar kudaden kasar waje, hakan yasa kamfanin jiragen saman kasar Spain ta dakatar da zirga zirgar jiragen samanta zuwa Najeriya, a yayinda kuma kamfanin jiragen saman Amurka da ake kira American Airlines tace itama zata dakatar da zirga zirgar jiragenta a wannan wata da muke ciki.
Kamfanin jiragen kasar Jamus dake Luftansa, tace yanzu haka ma akwai Dalar Amurka Miliyan 20 na kudaden tikiti da ta sayar a Najeriya, wadanda kuma ta kasa musanyasu daga Naira zuwa dalar Amurka, domin daukar kudaden zuwa kasashen su.
A wasikar da shugaban kungiyar kamfanonin jiragen sama na duniya ya rattabawa hannu, yace akwai bukatar gwamnatin Najeriya da ta girmama yarjejeniyar kasa da kasa da ya shafi zirga zirgar jiragen sama.