Bayan cika duk sharudan da babban bankin Nigeriya ya gindiya aka kafa bankin Jaiz, wanda ya zamo bankin farko na Musulunci a kasar.
Gabanin kafa bankin an kwashe shekaru aru-aru ana gudanar da irin wannan bankin a kasashen Birtaniya da Amurka.
Alhaji Mahe Abubakar mukaddashin babban daraktan bankin yace akwai malamai da yawa da suke da ra'ayi daban daban akan harkan bankin musulunci. Wasu yace akwai rashin fahimta, wasu kuma abun da suka karanta sun yi mashi wata fahimta daban.
Alhaji Mahe yace sun kirawo malamai daga kowane bangare daga kuma kowace darika domin a zauna a yi mukabala a samu mafita domin a samu hanyar cgaban bankin Musulunci a Najeriya.
Malam Ali Isa Pancani na cikin malaman da suka halarci taron yace malaman sun karu da juna game da alamuran da suka shafi tsarin bakin da bab ruwa a ciki. Yace an gabatar da bayanai kuma an fahimci juna. Sun yadda cewa duk wanda aka yiwa tambaya kan kowane lamura idan bashi da amsa kada ya yi gaggawar bada amsa. Ya tambayi wadanda suka dade suna bincike a kai.
Dr. Bashir Umar na masallacin limamin wani masallacin Juma'a dake Kano, kuma masani kan tsarin bankin da babu ruwa yana cikin wadanda suka taka rawa wajen kafa bankin Jaiz, yace a yayin taron a gano wani kalubale dake fuskantar bankin wanda yake bukatar kulawar mahukumta.
Ga karin bayani.