Batun tsaro dai yanzu haka yana zama wata babbar annoba musammam ma a arewacin Najeriya. Sanata Ndume ya ce a kididdigar da hukumar ci gaban al’umma ta MDD ta bayar na nuni da cewa jihar Borno tafi kowacce fama da talauci, kuma batun Boko Haram ya jefa jihar cikin halin kaka ni kayi.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka mafi yawan al’umma na zaune ne cikin garin Maiduguri, kuma da zarar karfe hudu na yamma ya yi za a rufe hanyoyin shiga da fice har zuwa karfe bakwai na safe. Wanda hakan ke nuni da cewa har yanzu akwai akwai matsalar tsaro.
Sanata Ndume ya ce Boko Haram yanzu haka ba wata barazana bace, an dai barta ne ta ci gaba a wasu wureren da jami’an tsaro sun riga sun san da zamansu, kamar yankin tafki Chadi da bangaren dutsen Mangara da kuma yankin Sambisa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum