Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IMO:Gwamna Emeka Ihedioha Ya Gabatar Da Manufofi 15 Na Inganta Jihar


Rantsar da gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha
Rantsar da gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha

Dubun dubatar jama'a ne suka halarci babban filin wasan Dan Anyiam dake Owerri, babban birnin jihar Imo, domin rantsar da tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Honarabul Emeka Ihedioha, a matsayin sabon gwamnan jihar Imo.

A jawabinsa na farko, Emeka Ihedioha ya shaida wa al'ummar jihar da kuma sauran jama'a da suka garzayo domin bikin cewa "Manufarmu ita ce mu sake gina Jihar Imo, mu sake fasalinta, mu kuma mayar da ita cibiyar ilimi, noma, masana'antu, yawon bude ido, al'adu, wasanni, nishadi, inganta baiwa, kimiya da fasaha, da kuma yin amfani da albarkatun kasarmu, don kirkiro damar raya tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar al'ummarmu."

Ihedioha ya dai bayyana kudurori kimanin 15 da gwamnatinsa zata cimma a cikin shekaru hudu masu zuwa, ciki har da samar wa matasa abin yi, da tallafawa mata, da samar da stabtataccen ruwan sha, da inganta ilimi, noma, tsaro, da dai sauransu.

Sashen Hausa ya yi hira da wadansu da suka halarci bukin rantsar da sabon gwamnan. Wani mai suna Okpara na cewa, "Ina son abinda ke faruwa yau. Kenan abin da muka roka, kuma shine abin da muke ta kokarin gani, wato kubutar da jihar Imo. Muna so a dama da talaka. Kuma mun san cewa a matsayinsa na gogaggen shugaba, Emeka Ihedioha zai dawo da martabar jihar Imo."

Al’umman jihar Imo sun bayyana fatar ganin al’amura sun gyaru da kuma fatar ba za a sake komawa gidan jiya ba. Sun bayyana bukatar ganin 'ya'yansu sun samu isasshen ilmi, kuma ya zamana duk aikin da za a yi a jihar ya zama na kwarai.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe

Rantsar da gwamnan Imo-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG