Jami’ai sun sanar da cewa Kakakin Majalisar Dokokin Somalia, Mohammed Osman Jawari, ya sauka daga kujerarsa bayan wani sa-in-sar siyasa da aka kwashe makwannin uku ana yi da Firai ministan kasar.
Ministan tsarin mulkin kasar, Abdirahman Hosh ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce kakaki Jawari ya mika takardar ajiye aikinsa.
Dan majalisa Hussein Arab ma ya shaidawa wakilin Muryar Amurka saukar kakakin daga kujerarsa, inda ya ce “ mataimakin kakakin Abdeweli Muddey ne ya karanto mana takardar barin aikin kakakin da safiyar yau”.
Daya daga cikin mukarraban Jawari ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya yi murabus din ne bisa zabin kansa.
Facebook Forum