Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Hungary Jam'iyyar Dake Kin Bakin Haure Ta Lashe Zaben Majalisar Dokoki


Firayim Ministan Hungary Viktor Orban wanda jam,iyyarsa ta lashe zaben majalisar dokokin kasar bata son bakin haure
Firayim Ministan Hungary Viktor Orban wanda jam,iyyarsa ta lashe zaben majalisar dokokin kasar bata son bakin haure

Sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin Hungary zai tabbatar da cewa babu wani bakon haure da zai ratsa kasar shiga nahiyar Turai

Firayim Ministan kasar Hungary Viktor Orban ya na murnar abin da ya kira gagarumin nasara ga Hungary, bayan jami’iyarsa mai manufar kin bakin haure ta Fidesz ta lashe kujerun majalisa masu yawa a zaben wakilan majalisar da aka yi jiya Lahadi.


Bayan kirga kusan dukkan kuru’un da aka kada, jami’iyar Fidesz da kawarta ta Christians Democrat ne ake sa ran zasu lashe kujeru 133 cikin kujeru majalisa199.


Jami’iyar masu kishin kasa ta Jobbik zata sanu kujeru 26, yayin da jami'iyar yan gurguzu zata samu kujeru 20.


Hungary ta gina Katanga kuma ta kaddamar da dokoki da nufin hana bakin haure daman ratsawa ta kasar zuwa kasashen yammacin Turai daga wurare kamar Syria da Afghanistan.


Amma kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana fargabansu ga yanda nunawa bakin haure kiyayya yayi tasiri a yakin neman zabe.

Koda yake galibin masu kada kuri’a, sun bayyana damuwarsu akan kaurar bakin haure, amma akasarinsu sun ce sun fi ra’ayi ko kuma shaawa akan yaki da cin hanci da rashawa da talauci da kuma inganta tsarin kiwon lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG