Wata kotu da ke zama a Abuja ce ta yanke hukuncin cewa Saraki ya fuskanci kuliya kan tuhumarsa da ake yi na ba da bayyana ba daidai ba bisa kadarorinsa.
Kotun da’ar ma’aikata ce ke tuhumar shugaban majalisar bisa zargin cewa ya yi karya wajen bayyana dukiyar da ya mallaka.
A wata takarda mai dauke da sa hanun mai magana da yawunsa, Saraki ya nuna takaicinsa bisa zargin yana mai cewa zai wanke kan sa a shari’ar.
Saurari karin bayani a wannan rahoto na wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda game da wannan lamari: