Yayinda Amurka ke goyon bayan kokarin kasar Turkiyya na gano wadanda suka yi yinkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba ranar 15 ga watan Yulin bana, rufe kafafen yada labarai da kuma kama wasu ‘yan jarida a karshen makon da ya gabata abin damuwa ne a cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Kamun babban editan kamfanin jaridar Cumhuriyet Murat Sabuncu da wasu manyan jami’an kafar ya zo ne bayan da aka dakatar da ma’aikatan gwamnati fiye da 10,000, da malaman makaranta, da jami’an kiwon lafiya ranar Asabar din da ta gabata. Haka kuma an rufe kafafen yada labarai fiye da goma a karshen makon.
Wani babban jami’in kasar Amurka ya fadawa manema labarai jiya Litinin cewa, abubuwan da suka wakana cikin karshen makon jiya abin damuwa ne, saboda yadda shugaban kasar Turkiyya ya shiga cikin harkokin zaben shugabannin jami’o’in kasar.