A jiya ne babban jami’ain ma’aikatar shara’a din, Peter Kadzik ya aika wata wasika zuwa ga manyan ‘yan Majalisar Dattawa na jam’iyyar Democrats da suka fusata da jin cewa an sake bude wannan binciken ana daf da gudanarda zaben shugaban kasa.
A ranar Jumu’ar da ta gabata ne dai shugaban FBI din, James Comey ya sanarda Majalisar Dokokin Amurka cewa suna duba wasu sababbin sakkonin email masu alaka da Hilary da aka gano a lokacinda ake gudanarda bincike akan wani tsohon dan majalisar dokokin Amurka mai suna Anthony Weiner, wanda kuma tsohon mijin Huma Abedin ne, wata mai yi wa Hilary Clinton hidimomi.
Tuni abokin adawar Hilary din a wannan zabe, Donald Trump na jam’iyyar Republican ya soma anfani da wannan sabuwar dama, wajen caccakarta da kuma yabawa shugaban FBI din kan daukan wannan sabon matakin na bude binciken.