Sai dai kuma Kerry zai tattauna da shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyata, kafin ya gana da ministoci wadanda zasu tattauna yadda za a shawo kan hana sabuwar kasar Sudan ta Kudu afkawa cikin wani sabon rikici.
Mutanen kasar ta Sudan ta Kudu dai, sun jima suna cikin halin 'ka 'ka na kayi. Kamar yadda wani babban jami'in harkokin waje ya shaidawa manema labarai.
Rashin kwanciyar hankali a kasar ta Sudan ta Kudu, ya haifarwa Miliyoyin mutane asarar matsugunnan su, kana aikin jin kai ya zame wani babban alkakai, wanda hatta kasashen duniya ma sun rasa ta yadda zasu bullo wa al’amarin.
Kasar Sudan ta Kudu dai ta jima cikin halin zamar dar-dar ne tun daga lokacin da suka samun yancin su daga kasar Sudan a cikin shekarar 2011.
Tun daga wannan lokacin ne rikici ya barke wanda ya haifarwa kasar yakin basasa.
Haka kuma Kerry, da sauran ministocin harkokin wajen kasashen Afirka ta gabas sun shirya tattaunawa akan kasar Somalia, wadda take hasashen ganin ta gudanar da zaben yan majilisar kasar dama na shugaban kasa wanda hakan na iya kawo musu zaman lafiya.
haka kuma a cikin wannan makon ne Kerry zai ziyarci Najeriya, inda zai tattauna da shugaban kasar wadda ‘yan ta'addar Boko Haram ta kashe sama da mutane dubu 20 tun daga shekarar 2009.