Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Sudan ta Kudu Zai Yi Jawabi daga Wurin Buyarsa


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Ana kyautata zaton madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar zai yi jawabi ta kafar radiyo daga mabuyarsa wadda magoya bayansa suka ki bayyanawa saboda dalilan tsaro

Wani kakakin kungiyar adawa ta SPLM-IO ta kasar Sudan ta Kudu yace a yau Alhamis ne tsohon madugun ‘yantawaye kuma tsohon mataimakinn shugaban kasar Riek Machar zai fito ya yi magana a karon farko a cikin lokaci mai tsawo tun bayanda ya boye a watan Yulin da ya gabata, lokacinda aka yi wata gwabzawa tsakanin mayakansa da na sojan gwamnati a Juba, babban birnin kasar.

A wancan lokacin ne shugaban kasar ta Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya kori Machar daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa inda kuma ya maye gurbinsa da Taban Deng Gai, wanda wani rukuni na kungiyar SPLM-IO ta Machar din ke baiwa goyon baya.

Dangane da haka ne a yanzu jami’in watsa labarai na kungiyar ta SPLM-I, Mabior Garang de Mabior, ya fito yau yana gayawa gidan rediyon nan na Muryar Amurka cewa yanzu an dauki Machar, an maida shi wata kasa inda daga can ne zaiyi hira da manema labarai. Yace dole su boye asirin wurin da tsohon mataimakin shugaban kasa yake saboda, a cewarsa, “makiya zaman lafiya” na ci gaba da farautarsa.

Sai dai kuma gwamnatin Sudan ta Kudu din ta musanta cewa tana neman hallaka Machar.

XS
SM
MD
LG