Amma batun na ciga da daukan hankalin 'yan kasar kamar su Abdu Alhaji Idi wani dan rajin kare dimokradiya.
Yace idan domin kishin kasa suka shiga kawancen ya kamata a ce lokaci ya yi da yanzu za'a yi yaki da cin hanci da rashawa da hana almundahana da duk wata munamuna saboda mutane sun azurta kasnu ta wadannan hanyoyin.
Jam'iyyar MODEN Lumana da aka kafa a shekarar 2009 bayan da baraka ta taso tsakanin shugabannin MNSD na wannan lokacin, wato Hamma Ahmadou da Tanja Mammadou itace babbar kawa a kawancen 'yan adawa har zuwa ranar da ta sanarda shirin ballewa.
Bala Ibrahim wani jigo a kungiyar matasan MODEN ya bayyana matsayinsu akan matakin.Yace su a MODEN Lumana dimokradiya suka sa gaba. Kowa nada 'yancin ya bi yadda yake so.
Amma kawancen 'yan babu ruwanmu na cewa babu wani koma bayan da ficewar MNSD daga kawancen zai haifar domin a cewar kakakinsu Hambali Dodo basu ji dadin irin kwane-kwanen da MNSD keyi ba. Idan basa son cigaba da yin adawa suna iya janyewa amma su, suna nan kan matsayinsu na 'yan adawa.
Duk da dalilan da MNSD ta bayar na amsa tayin goron shiga gwamnati da Issoufou Mahammadou yayi, Farfasa Issoufou Yahaya na jami'ar Yamai na ganin jam'iyyar MNSD na son ta dauki fansa ne akan wadanda suka guje mata can baya suka shiga gwamnati. Idan aka duba tafiyar kasa ana bukatar kwanciyar hankali a kuma barin duk wani jaye-jaye.
Shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya Bazum Muhammad ya jinjinawa jam'iyyar MNSD da yunkurin da tayi saboda yin hakan zai kara taimakawa gwamnati ta kara samun karbuwa a wurin masu hannu da shuni.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.