Haka nan Mr. Biden yana isa kasar a kuma dai dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka tallafawa kutsen da sojojin Turkiy ya yi cikin Syria. Mataimakin shugaban na Amurka tareda PM kasar Binali Yildrim zasu yi taro na hadin guiwa da manema labarai, bayan da ya gana da manayan jami'an kasar ciki harda shugaban kasar Rajib Tayyib Ergodan., a Ankara babban birnin kasar.
Mr. Biden shine wani babban jami'i a gwamnatin Obama kuma na hanun damansa, wand a galibi yake wakiltar fadar White House a harkokin difilomasiyya masu sarkakiya. Mataimakin shugaban kasar yayi suna wajen kulla dangantaka d a shugabannin kasashen duniya, ciki harda Erdogan, mutumin d Biden ya kira "dadadden abokinsa."
Yau Laraba, Erdogan ya sake nanata kira ga Amurka ta mika kasar malamin addinin Islaman nan dan kasar Fethullah Gulen wanda yake da zama anan Amurka dangane da zargin da kasar take yi masa cewa yana da hanu a yunkurin juyin mulkin da aka so ayi kasar wanda bai sami nasara ba. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fada jiya Talata cewa ta sami bukatar da Turkiyya ta gabatar na neman a mika mata malamin dan shekaru 75 d a haifuwa, amma bukatar bata fito fili ta nuna shaida irin rawar da Gulen ya taka a yunkurin juyin mulkin.
Jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka tace za'a yanek shawarar kan batun mika malamain ne tareda la'akari da shaidar da aka gabatar, da kuma irin sharuddan da suke kunshe cikin yarjejeniyr mikawa juna mutane da kasashen suke nema.