Yace akwai mutane da dama musamman mata da yara da suke matukar bukatar ruwan sha da abinci cikin gaggawa domin idan basu samu ba yawancinsu zasu rasa rayukansu cikin dan karamin lokaci.
Yace akwai fargaban fadawar hukumar agajin cikin hadari a wannan yakin da yanzu ya kwashi tsawon shekaru biyar ana zuda jini. Stephen O’Brien ya bayyanawa hukumar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a bayanansa na wata-wata akan irin halin da ake ciki.
Ya kara da cewa har iyau ba zai iya tabbatar da tsagaita wuta na awa 48 ba da bangarorin suka amince su yi don bada daman shigar da ma’aikatan agajin a yakin Aleppo su gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Tun cikin wancan watan ne Majalisar Dinkin Duniya take kira a tsagaita wuta na awa 48 a kowane mako a Aleppo don bada daman kai kayan taimako wa dubban marasa lafiya da masu fama da rauni
O’Brien yace Majalisar Dinkin Duniya a shirye take ta shiga da tireloli 70 dauke da kayan agaji a gabashin Aleppo nan da nan da ta samu tabbacin tsaron lafiyar ma’aikatanta.