Sai dai a wannan karon taron yazo a wani lokacin da waadin ‘yan majilisar na tsawon shekaru 5 ke cika, haka kuma aikin sun a wakilci a majilisar yazo karshe, sakamakon shank aye a zaben da akayi a watan jiya.
Dan majilisar dokokin kasa Zakari Umaru yana wakilci a karkashin jamiyyar PNDS tarayya.
‘’Akwai dokokin da gwamnati ta aiko wa majilisa musammam dokoki ne na furoje-furoje da wasu kadade wadanda masu hannu da shuni suka ba Niger ko kyauta ko kuma rance wadannan dokokin sune mafi yawan da suke hannun ‘yan majilisar, tunda za a sake zabe, tunda za a zabi shugaban kasa, an zabi ‘yan majilisa, kuma ko wace gwamnati tazo da nata tsari kenan soma aikin majilisa an dakatar dashi daga wannan dokokin gaggawa na kadaden da ake son su shigo aljihun gwamnati cikin lokaci, to amma sauran ayyuka da suka shafi tsari na kowane dan takara wannan wanda ALLAH yasa aka zaba nan da sati biyu shine zai tsara wasu dokokin da zai iso majilisa dangane da burin sa da kuma alkawurran da ya daukar wa ‘yan kasa.’’
A bisa la’akari da cewa ranar 6 ga watan Maris ne yakamata a kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na biyu, Amadu Sale na jamiyyar Model Lumana ta’yan adawa ya bayyana cewa basu ga anfanin kiran wannan taro ba.
‘’Muji tsoron ALLAH yanzu duk ‘yan majilisar dake anan da zaran an fara kanfe duk wucewa zamu yi wajen kanfe, to su wanene zasu zauna suyi aiki anyi dai ne domin ance muyi, amma batun tattaunawa zaiyi wuya.
Amma jamiyya mai mulki ta bakin Zakari Umaru dolea mutunta kundin tsarin mulkin kasa.
Ga Suley Mummnin Barma da Karin bayani