A jawabin da yayi ta bidiyo da kwamitin yakin neman zaben Mrs. Clinton ya bayyana, Obama yace yasan irin wahalar shugabanci, domin haka ne yasan cewa tsohuwar sakatariyar harkokin wajen da tayi aiki da shi, wacce tsohuwar uwargidan shugaban Amurka ce, zata iya tafiyar da wannan aiki.
"Hakika ma, bana jin akwai mutuniyar da ta cancanci rike wannan mukami, inji Obama. "Jaruma ce, tana da tausayi da karfin halin ganin aiki ya tafi yadda ya kamata."
Fadar White House tace Mr. Obama zai yi yakin neman zabe a karon farko tareda Madam Clinton ranar Larabna mai zuwa a jihar Wisconsin. Jihar da Obama ya lashe a duka zabukan shugabancin Amurka biyu da yayi takara.
Bayyana goyon bayan da yayi a hukumce, ya biyo bayan ganawa da yayi da Senata Bernie Sanders na tsawon sa'a daya, mutumin ya sami dumbin goyon miliyoyin Amurkawa musamman matasa.