Harin ta sama shi ne harin Houthi na farko a Isra'ila da ya fada tsakiyar birnin da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka, lamarin da ya yi sanadin tarwatsewar buraguzun karfe ta sama tare da baza gilasai a wani wuri mai fadi.
"Muna gudanar da bincike a yau da kuma kwanaki masu zuwa don fahimtar ainihin daga inda aka harba wannan barazana da kuma irin martanin da ake bukata don kare kasar da kuma irin martanin da za a mayar kan wanda ke barazana ga kasar Isra'ila," in ji Rear Admiral Daniel Hagari, mai magana da yawun sojojin Isra'ila.
‘Yan Houthi sun harba jirage mara matuka da makamai masu linzami zuwa Isra'ila tun bayan barkewar yakin kasar da Hamas.
Sai dai Isra’ilan ko kawayenta daga kasashen yammaci kan dakile hare-haren, illa na wannan hari na ranar Juma’ar.
Yahya Sare’e, kakakin Houthis, ya dauki alhakin kai harin a cikin wata sanarwa da aka buga a dandalin sada zumunta na X.
Ya ce harin na ramuwar gayya ne kan yakin Isra’ila da Hamas, kuma harin ya samu daya daga cikin wuraren da kungiyar ta kaikaita.
-AP
Dandalin Mu Tattauna