WASHINGTON, D. C. - Hakan na iya kara musu kaimi a hare-haren da suke ci gaba da kai wa jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya da kewaye da magudanar ruwa a kan madogaran yakin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza
Rahoton na kamfanin dillancin labaran kasar RIA Novosti ya ambaci wani jami'in da ba a bayyana sunansa ba amma bai bayar da wata shaida kan ikirarin ba. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Moscow ke ci gaba da nuna adawa da manufofin ketare na yammacin Turai a daidai lokacin da kuma take ci gaba da yakar Ukraine.
Sai dai kuma, ‘yan mayakan Houthi sun kwashe makonni suna yin ishara da "mamaki" a yayin da suke shirin amfani da shi a fadace-fadacen da ake yi a teku domin tinkarar Amurka da kawayenta, wadanda kawo yanzu suka iya kakkabo duk wani makami mai linzami ko kuma jirgin da bama-bamai da ya zo kusa da jiragen yakinsu a a tekun gabas ta tsakiya
Babbar mai taimaka wa Houthis, Iran, ta yi ikirarin cewa tana da makami mai linzami mai matukan karfin kuma ta bai wa 'yan tawayen makamai masu linzami da suke amfani da su am a yanzu.
Ƙarin irin wannan makamin cikin makamansu na iya haifar da babban ƙalubale ga tsarin tsaron sararin samaniya da Amurka da kawayenta ke aiki da su, ciki har da Isra'ila.
Yan kungiyan Houthi "na son fara kera shi don amfani da shi a lokacin hare-hare a tekun Bahar Maliya da Tekun Aden, da kuma kan hare-hare a Isra'ila."
-AP
Dandalin Mu Tattauna