Yanzu mayakan Boko Haram sun dau sabon salon kai farmaki kauyukan da babu hanyar sadarwa, sannan kuma suke da sarkakiyar shiga a wuraren da aka koma na kananan hukumomin Michika da Madagali da ke kusa da dajin Sambisa dake zaman shelkwatar mayakan Boko Haram.
Harin baya bayan nan shine na dirar Mikiyar da suka yiwa kauyen Kamale da ke karamar hukumar Michika inda suka kashe mutum hudu da kuma sace dukiya. To amma kuma ba kowa ya sani ba, sabili da matsalar rashin hanyoyin sadarwa.
Cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya har da wani dan majalisar wakilan Najeriya, Mista Adamu Kamale da ke wakiltar mazabar Michika da Madagali, wanda sai da ya buya ta hanyar kwana akan duwatsu.
Rundunan 'yan sandan jihar Adamawan ta tabbatar da wannan sabon harin inda ta bukaci jama’a da su zama masu kulawa da ankara don kaucewa fadwa tarkon 'yan kungiyar ta Boko Haram. Kamar yadda Kakakin 'yan sandan jihar Othman Abubakar ya bayyana.
Facebook Forum