Jerin farko na iskar ta taho da dusar kankara wacce ta ratsa tsakiyar yankin na Atlantic dake gabashin Amurka cikin dare zuwa safiyar Alhamis din nan.
Ana hasashen iskar zata fi shafar yankin arewa maso gabashin Amurka.
Inda ake tsamanin zata zubar da dusar kankara fiye da centimita 20 a birnin Boston dake jahar Massachussets, ina a yau aka rufe makarantu kaf a saboda yawan dusar kankara.
Haka nan ana jin iskar mai karfin gaske zata ratsa yankin bakin gabar teku a yankin arewa maso gabashin Amurka har zuwa kasar Canada. Haka nan kuma ana gargadin yiwuwar a fuskanci mummunar iska da kankara a garuruwa dake kan gabar teku daga jahar Virginia har zuwa Maine.
Masu nazarin yanayi, sun kira iskar "bomb" saboda yadda cikin dan karamin lokaci sa'o'i 24 a sami koma bayan yanayi, wadda ya janyo guguwa mai karfi.
A halinda ake ciki kuma mummunar yanayi na hunturu, ya janyo kankara, da sanyi mai tsanani a sassan da basu saba fuskantar irin wannan yanayi ba.
Facebook Forum