Gwamna Rauf Aregbesola, ya bayar da tabbacin kafa kwamitin ne unguwar Sabo Ile-ife, lokacin da ya raka tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da ya kai ziyarar jajantawa ‘yan Arewa game da abin da ya faru da kuma asarar da suka yi a rikicin.
Aregbesola, ya ce a matsayinsa na gwamna zai kafa kwamitin da zai binciko sanadiyar tashin hankalin da ya faru da nemo masalaha da kuma taimakawa mutanen su rage radadin asarar da su ka yi. Gwamnan ya ce jami’an tsaro sun damke wasu mutane 20 da aka zargi da laifin kisa da lalata dukiyoyi.
Da yake magana da manema labaru Sanata Kwankwaso, ya ce yazo ne biyo bayan rigingimun da suka faru a garin Ile-ife wanda yanzu haka an riga an shawo kan su, yasa ya kawo ziyara domin jajantawa ‘yan Arewan da iftila’in ya afkawa.
Haka kuma ya yi alkawarin cewa gidauniyarsa ta Kwankwasiya za ta taimakawa mutanen da suka yi asara.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.
Facebook Forum