Haka kuma kwamitin zai yi aikin sasanta duk wata matsala, ko rashin fahimtar juna da ka iya kawo fituna tsakanin kungiyoyin addinai masu banbancin ra’ayi.
A shekarun baya dai gwamnatin jihar ta fatattaki mutanen Darul Islam, da sukayi kokarin kafa daular musulunci a yankin karamar hukumar Makwa da kuma ‘yan kungiyar Islahuddeen a yankin Mashego.
Baban Darakta a ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar Neja, wanda kuma shine shugaban kwamitin, Sheikh Umar Faruk, yace kasancewar an san jihar Neja da zaman lafiya hakan yasan gwamnatin jihar ta baiwa zaman lafiya muhimmanci. Hakkin wannan ma’aikata ne mai lura da harkokin addinai ta tare duk kofar da rikicin addini zai bullo.
Daya daga cikin mambobin kwamitin Mohammad Aliyu Isah, kuma limamin masallacin Juma’a a jihar, yace fahimtar juna tana da muhimmanci a aikin samar da zaman lafiya a jihar Nejan.
Cikin mako mai zuwa ne gwamnatin jihar Neja zata kafa irin wannan kwamiti da zai yi aiki a bangaren mabiya addinin krista.