Manufar taron ita ce lalubo dabarun dakile aukuwar tashin hankali da tarzoma a cikin al'ummar Najeriya, musamman abun da ya shafi addini.
Taron ya tattaro malaman addinin musulunci daga sassa daban daban na kasar. Daya daga cikin malaman daga Kano limamin masallacin Shehu Tijjani Muhammad Nasir Adamu yace sai an kula da yadda ake aika sakwanni a wajen wa'azi. Malamin da bai san abun da yakamata ya ce ba ya zo ya cabawa mutane ya turasu cikin jeji. Yace ba kowane malami za'a bari yayi wa'azi ba sai wanda ya kosa kuma yana da fahimma mai kyau.
Shaikh Adamu ya cigaba da cewa dole a san yadda za'a taimakawa yara maza da mata da tunanensu saboda yadda mutane ke muamala da naurorin zamani akwai bayanai da kowa zai iya samu.Ya kira a shirya yadda za'a tunkari cigaba dake doso al'umma.
Shaikh Karimunla Kabara ya nuna damuwar cewa fitina a Najeriya kan faro ne daga karamar kura. Ya kira hukumomi da zara sun ga alamun wata kura to su hanzarta su dakileta. Shehunan malamai kuma su yi kokarin wayar da kawunan matasa.
A wani gefen kuma Shaikh Adamu Muhammad Dokoro na nuna rashin hikima ga dabarun musulunci kan kudurin daidaito tsakanin maza da mata dake gaban majalisar dattawan Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.