Daidai lokacin da a ke samun karuwar tashoshi musamman masu amfani da harshen Hausa a tauraron dan adam, kungiyoyin addini, tare da kungiyoyin kawo hadin kai, na zuba jari a tashoshin don yada tarbiyya da kare kyawawan al’adu.
Baya ga tashar Hausa 24 da ke Saudiyya, Afirka 3 a Sudan, SunnahTv da MANARA a Jamhuriyyar Nijar, kungiyar JIBWIS mai hedikwata a jihar Jos ta kaddamar da sabuwar tasha mai taken AL-IRSHAAD da za ta rika yada shirye-shiryenta akan tauraron STARTIMES.
“Ina fata tashar za ta rika yada labaran raya ilimi da zamantakewar al’umma kan lamuran yau da kullum” inji shugaban kamfanin STARTIMES Mr.Tochua.
Sheikh Sani Yahaya Jingir, wanda shi ne shugaban majalisar malamai na kungiyar ta JIBWIS, ya ce tashar za ta maida hankali kan shirye-shiryen tabbatar da salama.
Baya ga ‘yan majalisar dokokin Najeriya da su ka halarci taron kaddamarwar a Abuja, Sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa ya zama uban taro.
“Mu na murna da kafa wannan talabijin, saboda za ta wayar da kan jama’a a kan musulunci.
Alhaji Idris Musa ya bukaci tsayawa kan manufofin kafa tashar don samun nasarar sakon wa’azi da zaman lafiya tsakanin al’ummar Najeriya.
Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Saleh Shehu Ashaka.
Facebook Forum