Bayan kwashe tsawon kwanaki ana ganawa tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tawagarsa da ta Sarki Bin Salman na kasar Saudi Arabiya. An samu cinma matsaya don ganin kasar ta Saudiyya ta tallafawa kasar ta Najeriya.
A wata tattaunawa da Muryar Amurka ta yi da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Fasaha Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami, daya daga cikin tawagar Najeriya, ya shaida cewar an samar da matsaya ta yadda kasashen biyu zasu yi aiki hannun da hannu, musamman wajen bunkasa matatun mai da ake da su a Najeriya, don su gudanar da aiki yadda ya kamata.
Haka kuma an cinma matsaya akan wannan taron za’a dinga gudanar da shi a kowacce shekara, don Najeriya ta bayyana inda take bukatar taimako, ita kuwa kasar Saudiyya a shirye take don ta taimaka.
Ya kuma kara da cewar, za’a inganta hanyoyin sadarwa da ake da su a Najeriya don daukaka darajarsu suyi dai’daito da na sauran kasashen duniya. Kana Kasar za ta taimaka wajen ganin an tallafawa manoma don gudanar da noman zamani.
Haka kuma Najeriya a yanzu ta gayyaci kasashe biyu Saudiyya da Rasha duk a cikin ‘yan kwanankin nan don su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, kuma Najeriyar za ta ci gaba da neman sauran kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya don shigowa kasar su saka hannun jari.
Don bukatar karin bayani sai a saurari cikakkiyar tattaunawar cikin sauti.
Facebook Forum