A Jamhuriyar Nijer yayin da majalisar dokokin kasa ta fara zaman taronta a yau domin nazarin wasu kudirorin dokar da gwamnatin kasar ta gabatar, ‘yan adawa sun nuna rashin jin dadinsu da jawabin shugaban majalisar Ousseini Tinni.
‘Yan adawa sun ce shugaban majalisar ya karkatar da jawabinsa akan wasu batutuwa kamar na yi wa majalisar kwalliya a maimakon halin kuncin da tallakawa ke ciki.
Daga cikin korafe-korafen da ake ta batu a kasar ta Nijar a ‘yan kwanakin nan, sun hada da korafin sabuwar dokar harajin 2018.
Sanna daga cikin kudurorin da gwmnatin ta gabatar, akwai dokar aikin alkalan shari’a da dokar aikin ma’aikatar shige da ficen kaya.
Amma masu rin jaye a majalisar sun ce sai an yi nazari kafin su yi magana akan batutuwan.
“Duk abinda gwamnati ta yi a lokacin da ba ma nan, idan dai bisa harkar ka’ida ne, dole sai an gamu a maido shi nan, an tattauna an bincika an ga yadda ya kamata a yi.” Inji Shittu Mamane, dan majalisa a bangaren masu rinjaye.
Sai dai, jawabin na shugaban majalisar a cewar ‘yan adawa, bai gamsar da su ba domin bai tabo inda yake yi wa ‘yan kasar kaikayi ba.
“Kasafin kudi ya sa talakawa suna ji a Nijar, wane tsari ne ya kamata mu ‘yan majalisa ya kamata mu dauka mu share masu hawaye? Inji Kakakin ‘yan majalisar, Sumana Sanda.
Facebook Forum