Daruruwan mata sun yi dafifi a ofishin Hukumar da ke kula da sasanta jama’a a jamhuriyar NIJER inda suka bukaci hukumar da ta sa baki domin ganin ma'aikatar ministan ilimi a matakin firamare ta soke matakin aika wasu matan aure malaman kwantiragi zuwa wasu sassa dabam, da nufi rage cinkoson malamai a Yamai.
Kimanin malamai dubu biyu ne ke zaune ba su da ajin koyarwa.
Shugabar kungiyar malaman kwantiragi mata, Fatimata Isaka ta ce,
"Mu uwaye ne don haka ba za mu yarda mu bar 'ya'yanmu ba, shi ya sa mu ka kawo kukanmu nan."
Bayan wata ganawa ta 'yan mintoci kadan, da shugabannin kungiyar malaman kwantiragi mata, Shugaban Hukumar da ke sasanta 'yan kasa, Malam Ali Sirfi ya karbi korafin a hukumance sannan ya gindaya musu wasu sharudda masu alaka da tsarin aiki.
Darektan ofishin babban jami'in hukumar ta Mediature, Alhaji Moustapha Kadi Oumani yace, ya kamata mata sun dakatar da zaman dirshan da suke yi domin su jira su ga yadda abubuwa za su kasance bayan hukumar ta gana da sauran hukomomin da ke jayayya tsakaninsu.
Za su kuma nemi ji ta bakin ministan ilimi da kansa domin samun maslaha.
A makon da ya gabata malaman mata sun kai kukansu ga shugabannin kungiyar malaman addinin Islama ta IEN akan neman a sauya wannan matakin mayar da su wasu wurare dabam da nufin rage cinkoso.
Sai dai alama haka ba ta cimma ruwa ba yayin da wa'adin da gwamnatin ta diba wa malaman da wannan mataki ya shafa domin komawa sabbin wuraren aiki ke cika a ranar 5 ga watan Maris.
Saurari cikakken rohoton Sule Moumini Barma
Facebook Forum