Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Dake Afirka, AFRICOM, Sun Kashe Mayakan al-Shabab


Wasu mayakan Al-Shabab
Wasu mayakan Al-Shabab

Cikin farmakin da rundunar sojin Amurka dake nahiyar Afirka ko AFRICOM ta dinga kaiwa kan mayakan al-Shabab a Somalia ta kashe wasu mayakan tare da jikata wasu da dama

Rundunar sojojin Amurka a nahiyar Afrika ta ce ta kashe mayakan al-Shabab guda biyu kana ta raunata wasu a wani farmaki ta sama da ta akai a kudancin Somalia.
Rundunar da ake kira AFRICOM a takaice, ta ce ta kai farmaki ta saman ne a ranar Litinin a kusa da garin Jilib dake tsakiyar yankin Jubba


Wannan shine farmaki na hudu a Somalia da rundunar sojin Amurka ta kai a cikin wannan shekara. A baya, Sojojin sun kai farmaki a kan al-Shabab a ranakun biyu ga watan Janairu da 18 da kuma 19 ga watan Faburairu.


A halin da ake ciki, mayakan al-Shabab guda goma suka gudu daga wurin gyara halayensu a garin Garowe a daren Lahadi, a cewar jami’an tsaro suna fadawa sashen Somalia na Muryar Amurka.


Mutanen sun gudu ne da misalin karfe takwas na dare agogon kasar, yayin da 'yan ta’addar suka haura katanga suka sulale cikin duhu a cewar majiyar.


Jami’ai a yankin Puntland sun ki magana ga 'yan jarida a kan gudun da mutane suka yi, amma majiyar ta fadawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa, shugaban wannan yankin Abdiweli Mohamed Ali Gas ya bada umarni a gudanar da bincike.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG