Babban jami'in gudanar da taron, dan Majalisar Tarayya daga jahar Arkansas Steve Womack, yayi maza ya gudanar da kuri'a kan batun, sannan ya ayyana cewa yinkurin bai yi nasara ba.
Rudun da aka gani a cikin dandalin taron, ya yi kama da rudanin da ke kan tituna a waje, inda daruruwan magoya bayan Trump da masu adawa da shi su ka yi ta gudanar da gangami da tazarar kilomita daga juna, bayan da aka bude wannan babban taron tabbatar da dantakara na jam'iyyar Republican, wanda za a yi kwanaki hudu ana yi jiya Litini a birnin Cleveland na jahar Ohio.
An tsaida cewa za a fi maida hanali ne kan batun tsaro da shigowar bakin haure a ranar farko ta taron.
Wadanda su ka yi jawabai a wurin taron sun hada da gwamnan jahar Texas da ke kan iyaka Rick Perry, da mahaifiyar daya daga cikin Amurkawan nan da aka kashe a Benghazi, na kasar Libiya, da 'yan rajin garanbawul ga batun shigowar baki, da tsohon Magajin Garin New York Rudy Giuliani, da matar Trump, Melania da sauransu.
Wani magoyin bayan Donald Trump mai suna Johanna Buletin, wanda ya yi tattaki daga jahar Tennessee zuwa Cleveland, ya ce wadanda basu goyon bayan Trump ba 'yan ra'ayin rikau na hakika ba ne.
Dambarwa ta barke a babban taron tabbatar da dan takarar Shugaban Amurka karkashin jam'iyyar Republican
Dambarwa ta barke a babban taron tabbatar da dan takarar Shugaban Amurka karkashin jam'iyyar Republican, 'yan sa'o'i da fara taron jiya Litini, bayan da masu adawa da mai jirar ayyana shi dan takara Donald Trump, su ka yi ta daga muryar bayyana rashin jin dadinsu da kin a sake barin wakilan zabe na delegates su kada kuri'a a dandalin taron.
WASHINGTON D C —
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024