A wani yunkurin ganin sun tilastwa shugaba Joseph Kabila sauka daga karagar mulki. A karshen shekerar nan wa’adin Kabila na biyu zai cika.
A makon da ya gabata jam’iyun suka dunkule a kasar Belgium, kuma sun hada da Jam’iyun UDPS da madugun ‘yan adawa Etienne Tshisekedi ke jagoranta.
Da kuma jam’iyar Dynamic Opposition, da kuma ta G7 da suka tsayar da gwamnan Lardin Katanga, Moise Katumbi a matsayin dan takararsu.
Baya ga haka akwai kungiyar Alternative 2016, wanda Vidiye Tshimanga ne mataimakin shugaba.
Bangaren ‘yan adawan kasar Jmahuriyar Dimokradiyar Congo, ya sha fama da matsalar rashin hadin kai.
Bisa misalin tun daga shekarar 1960, Vital Kamerhe, shugaban jam’iyar UNC bai halarci taron na Blegium ba.