Yau Alhamis Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi shelar baratar kasar Liberiya daga cutar Ebola, bayan da kasar ta yi nasarar shafe kwanaki 42 ba tare da jin duriyar wannan mugunyar cuta mai kisa ba.
"WHO ta yaba ma gwamnati da mutanen Liberiya saboda kwaggwaran matakin da su ka dauka kan bullar Ebola ta baya-bayan nan," a cewar wakilin WHO a Liberiya Dr. Alex Gasasira, wanda ya kara da cewa, "WHO za ta cigaba da taimaka ma Liberiya a kokarinta na kawarwa da ganowa da kuma daukar mataki kan duk wani yanayin da ba ta gane masa ba.
Wannan ne karo na hudu, tun bayan bullar wannan annobar, da aka ayyana Liberiya a matsayin wacce ta barata daga cutar. Na baya-bayan nan wata mata ce wadda ta kamu da cutar a kasar Guinea kafin ta taho Libreiya da 'ya'yanta, wadanda su ma su ka kamu.
Ya zuwa lokacin da WHO ta yi shelar kawo karshen yaduwar cutar Ebola a karshen shekarar bara, cutar ta hallaka mutane sama da 11,000 a uku daga cikin kasashen Afirka Ta Yamma da su ka fi kamuwa da cutar.