Jamhuriyar Kamaru ita ma ta shiga jerin sauran kasashen duniya domin gudanar da bikin ranar mata a hukumance.
Ministar walwala da jin dadin mata Mary Peres Adena Unduwa ta bayyana dalilin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta tsayar da ranar. Tace ana son mutane su gane cewa a ma'aikatan gwamnati da ma na masu zaman kansu yakamata mata suna da kaso hamsin cikin dari amma mata basa samun ko kashi ashirin yayinda maza ke samun nasu kason har ma fiye da kowa.
Liman Danladi Ayuba limami a birnin Yaounde kuma a matsayinsa na wakilin musulmai musamman yayinda gwamnati ta kira musulmai da kiristoci su daidaita alamuran mata, yace ba haram ba ne mata su yi cudanya da mata saidai dole su kaucewa abun da haram ne a musulunci.
Ita ma Hajiya Tanko Tela bukin na yau na mata wanda ya hada kowa da kowa. Saidai matan hausawa a kasar ta Kamru basu taba samun komi ba daga gwamnati injita
Ga karin bayani