Jihohin da lamarin ya shafa sun hada da Bauchi a arewa maso gabas, sai Zamfara a arewa maso yamma, kazalika Ogun da Lagos a kudu maso yamma da kuma Abia da Imo a kudu maso gabas.
A sakon kar ta kwana, mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa Sanata Lawwali Shu’aibu, ya bada tabbacin dage zaben a jihohin shida.
Zuwa yanzu dai za a ce a na jiran sakamakon zaben fidda gwanin na jihohin da su ka kammala kada kuri’a, wa imma ta amfani da wakilai ko zaben ‘yar tinke.
Wakilan akasarin ‘yan takara a Bauchi sun yi watsi da batun yunkurin wasu na gudanar da zaben fidda gwanin ba tare da isowar jami’an APC daga Abuja ba.
Alhaji Sani Garba Agogo, ya ce su na nan su na jiran jami’an zaben kuma batun an yi zaben farfaganda ne.
Shi kuma Alhaji Hassan Sharif ya ce masu kalubalantar gwamnan a zaben ‘yan siyasar bariki ne.
Can Yobe inda APC tuni ta dau matsaya kan takarar Mai Mala Buni, PDP mai adawa ta tsayar da Ambasada Umar Damagum don kalubalantar APC a ranar babban zabe.
Can Imo tsamar na tsakanin gwamna Rochas Okorocha ne da ke son tsayar da surukin sa don ya gaje shi, inda mataimakin sa Eze Madumere da ya kwato kujerar sa a kotu bayan an tsige shi ke cewa a’a sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi
Lagos ma dai an samu sabani tsakanin gwamna Akinwummni Ambode da uban APC Bola Tinubu da hakan ke sanya takarar gwamnan karkashin APC a garari don Tinubu ya mara baya ne ga Sanwo-Olu da ya ce shi zai dawo da Lagos kan turba.
Shugaba Buhari wanda tuni ya zama dan takarar shugaban kasa na APC ba hamaiya bayan saya ma sa fom din takara Naira miliyan 45, ya bukaci jam’iyyar ta tabbatar da adalci a zaben fidda gwanin da yawanci ‘yan jam’iyyar ke ganin hanyar ‘yar tinke ne mafita.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum