A zantawa da sashen Hausa na Muryar Amurka jim kadan bayan kammala taron bikin maraba da sabbin dalibai na shekarar karatu ta bana su kimanin 1,000, shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribado, ya ce ana ci gaba da gudanar da tattaunawa tsakanin hukumar Jami’ar ta Jigawa.
Tattaunawar na gudana da hukumomin ilimi na kasar Gambia da kuma ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya domin karkare yarjejeniyar kasa da kasa ta bai wa daliban na kasar Gambia guraben karatu.
Farfesa Abdullahi Yusufu Ribado, wanda shi ne sakatare Janar na kungiyar Jami’o’in nahiyar Afrika ta yamma, ya fayyace alfanun da Jami’o’i ke samu daga kungiyar, ciki har da Jami’ar Jigawa da ke Kafin-Hausa.
A cewar Farfesa Ribado, Jami’arsa ta yi fice a taron mahawara tsakanin daliban wasu daga cikin Jami’o’in nahiyar Afirka.
Ita kuwa Jami’ar tarayya da ke Dutse fadar gwamnatin Jigawa ta ce a bana ta dauki rukunin farko na daliban da za su koyi aikin likita, kamar yadda shugabar Jami’ar, Farfesa Fatima Batulu Mukhtar, ta bayyanawa Muryar Amurka.
Sai dai duk da samuwar Jami’o’i guda biyu kusan lokaci guda a jihar Jigawa, har yanzu akwai dinbin daliban Jihar da ke kokawar samun guraben karatu a Jami’a.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum