Wannan bukata na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan Najeriya ciki har da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ke ganin ya kamata Buhari ya ja baya ya bar wa matasa.
A cewar gwamna Sani Bello, shugaba Buhari ya fito da Najeriya daga cikin wani hali kuma shekaru hudu ba za su isa ba, domin idan ya bari duk ayyukan da aka fara gudanarwa za a samu koma baya.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne a lokacin da wasu daruruwan mutane daga Kontagora suka kai masa ziyarar nuna goyon baya.
Da yake magana, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan yankin, Yusuf Magudu, ya ce sun goyi bayan matsayin gwamnonin amma akwai bukatar ganin kwamitin sasanta ‘ya‘yan jam’iyyar APC na Bola Tinibu, ya je jihar Neja.
Zargin rashin tabukawa wajen samar da ababen more rayuwa daga gwamnatin APC ya sa wasu ke neman dawowa daga rakiyarta.
Amma tsohon kwamishinan kudi a jihar Neja, Alhaji Mu’azu Bawa Rijau, ya ce rashin sani ne ya kawo zargin.
A yanzu dai ta bayyana cewa sai bayan zaben shekarar 2019 ne za a canza sabbin shugabannin jam’iyyar APC a Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum