Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jihar Filato


Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato
Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato

A kokarin da suke yi na ganin sun samar da tsaro a yankunan jihar Filato da ke fama da tashe-tashen hankula, rundunar sojojin Operation SAFE HAVEN da hadin gwiwan rundunar Operation HAKORIN DAMISA IV sun samu tarwatsa wani wurin kera makamai.

Hakan na zuwa ne a yayin wani aikin share fage a kan tudun mun tsira inda aka gano wani keɓaɓɓen gini wanda ya zama masana'antar kera makamai da ke kan wani babban fili a ƙauyen Pakachi, cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

A yayin aikin, an gano muggan makamai da na’urori masu alaka da su, tare da kuma kama wani wanda ake zargi.

Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato
Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato

An kama Mr. Tapshak Plangji, wani matashi mai shekaru 25 da haihuwa, wanda ake zargin yana da hannu wajen aikata haramtattun ayyuka a masana'antar.

Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Captain Oya James, a wata sanarwa ya ce wanda ake zargin shine ya mallaki masana'antar kera makaman wani Mr. Nuhu Meshack, wanda a halin yanzu yana nan a hannu ana kuma kokarin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato
Sojoji Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Jahar Filato

Sanarwar tace kayayyakin da aka kwato daga wurin sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda 5, mujallu kirar AK 47 guda 4, harsashi 11 na 7.62mm, albarusai 5mm da 9mm, bindigogi 21, bindigogin revolver 4, bindigogi 11 mai mujallu 5, gungun bindigogi mai jigida 17 na 0.44 incin ammonium, silinda carbide tare da Na'urorin haɗi.

Zarto guda 3, Filing Machines 12, guduma guda 4, injin tono 6, na'urar samar da wutar lantarki guda 2, G-Clamps 2 da Injin na feshi guda 1.

Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin Mr. Plangji, tare da bindigogin da aka kwato da sauran kayayyaki, a halin yanzu suna hannun rundunar domin ci gaba da bincike.

Wani gidan kera makamai a Jihar Filato
Wani gidan kera makamai a Jihar Filato

Rundunar sojin tace wannan nasarar da ta samu ya nuna jajircewar sojojin tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci a tsakanin al’umma.

Har ila yau, ta ce nasarar ta nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’ummar yankin wajen kare al’umma daga barazanar da ke tattare da kera makamai da safarar miyagun kwayoyi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG