Hadarin harin da tsautsayinsa Allah kadai ya san iyakarsa.
Sabili da abun da ya faru ya sa JNI ta kira al'umma da babbar murya su kuru su yi hankali kuma su bude idanuwansu. Na daya bangaren limmamai da kwamitin masallatai da manyan unguwanni da dattijai, maza da mata da yara lallai ya zanto wajibi a zauna a dinga tattauna harkokin da suka shafi tsaro domin wai sun zama 'ya'yan bora. Idan an tabasu ko an kashesu kamar ma su ba komi suke ba. Har yau ba'a kama ko a yanke hukunci akan wani wanda yayi wannan ta'asar ba.
Tun da gwamnati ta gagara to al'umma ba zasu zauna kara zube ba. Dokoki ma sun tabbatar cewa mutum na iya daukan kariya a kansa. Sabili da haka dole ne a zauna a tattauna domin su dauki matakan da su ma zasu iya kare kawunansu ba sai sun danganta ga gwamnati ba.
JNI bata ce a yi tashin hankali ko hatsaniya ba. Tattaunawa ce za'a yi a ga wacce hanya za'a bi. Kowacce unguwa ko lardi ko yanki yakamata a san abun da za'a yi kamar yadda ake shirya harkoki na 'yan banga lokacin da rashin tsaro ya addabi mutane.
Dangane da wadanda suka alakanta harin na Kano da kiraye kirayen da shugabannin JNI da ma sarkin Kano suka yi na cewa lokaci yayi su tashi su kare kansu sai suka ce babu gudu babu kuma ja da baya. Ma'ana, suna nan kan bakansu. Kowa ya tashi ya kare kansa da kansa. Al'umma idon kowa ya bude. Malamai, limamamai, attajirai, 'yan kasuwa dattawa har 'yan keken napep da kowa da kowa ya zamanto ido ya bude kuma akwai basira. Ba'a shiru duk inda aka ga lugu-lugu to a duba a gani. Wannan karon zasu samu warakar al'amuran idan Allah Ya yadda.
A bude ido a ga kai da kawowan mutane ta haka za'a san ko wanene, me ya keyi. Yin hakan yana da mahimmanci kwarai da gaske.
Ga rahoton Muhamud Ibrahim Kwari.