Shaikh Khalil Usman Khalil Albukurawi wanda ya jagoranci wa'adin bana a jihar Oyo shi yayi kiran a madadin kungiyar ta kasa a wajen rufe wa'azin a masallacin katako dake Unguwar Bodija dake Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo.
Yace kungiyar tace a tunatar da jama'a cewa lokacin da suka dangwala yatsunsu ga kuri'unsu to sun ce ga amanar addinisu sun ba duk wadanda suka zaba. Sun basu rayukansu da jininsu tun daga kan shugaban kasa har zuwa kasa. Sun bayar da amanar addininsu tare da amanar dukiyarsu. Duk wata rayuwa tasu ta zama amana a hannun shugaban kasa da gwamnonin jihohi da 'yan majalisu.
Kungiyar IZALA tace zasu zama manya manyan azzalumai idan basu cigaba da taimakawa shugabannin da addu'a ba. Wajibi ne su kaskantar da kansu fiye da da musamman a wannan karshen watan Ramadana. Su roki Allah ya taimaki shugaban kasa shugaba Buhari da mataimakinshi da gwamnonin jihohi Allah ya basu ikon sauke nauyin da jama'a ta dora masu cikin aminci.
Ya yi addu'a da fatan Allah ya dawo da tattalin arzikin Najeriya fiye da yadda yake da can. Ya zama fiye da lokacin Yakubu Gowon da na Sardauna da Tafawa Balewa.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.